AU

Taron Kungiyar Afrika kan Yunwan kasashen Gabashin Afrika

Yau shugabanin kasashen Afrika ke gudanar da wani taro a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, dan kadadmar da gidauniyar taimakawa kasashen Gabashin Afrika dake fama da bala’in yunwa sakamakon fari.Shugaban gudanawar kungiyar, Jean Ping, ya bukaci shugabanin su bada gudumawa dan ceto rayukan abinda ya kira Yan’uwanmu maza da mata.Ana bukatar Dala biliyan biyu da rabi, dan samarwa mutanen Somaliya, Kenya da Habasha abinci.