Libya

An baiwa dakarun Gaddafi wa'adin ranar Asabar

Mustafa Abdel Jalil
Mustafa Abdel Jalil REUTERS/Esam Al-Fetori

‘Yan tawayen kasar Libya, da kuma ke rike da akasarin kasar, sun baiwa dakaru masu biyayya ga Shugaba Gaddafi nan da ranar Asabar, ko dai su mika wuya ko a musu luguden wuta. Shugaba majalisar gudanmarwan kasar, Mustafa Abdel Jalil, ya ce wannan wa’adin na matsayin goron sallah ga sojojin na Gaddafi, kuma in ba su yi amfani da shi ba, za a dauki matakan soja kan su.A halin da ake ciki kuma, ‘yan tawaen sun ce daya daga cikin ‘ya ‘yan Gaddafi, Saadi yaa yarda ya mika wuya.