Jamus

kamfanin Mota na Volkwagen ya yi rawar gani

kamfanin Volkswagen ke nan
kamfanin Volkswagen ke nan (Photo : Reuters)

An bayyana kamfani kera motoci na kasar Jamus Volkswagen, wanda kuma shine mafi girma a turai, a matsayin wanda ya fi kowane kamfanin kera mota rawar gani a duniya. Wani biciken da aka gudanar, ya dora Volkwagen a gaban abokan gasar shi, wato General Motors da Toyota, bayan da aka gano su biyun suna da matsaloli.Wannan kuma ta sa kamfanin ke fatan zama wanda ya fi kowane yawan motocin da yake kerawa, nan da shekarar 2018.