US

Amirka Na Fargaban Harin Ta'addanci

Magajin garin New York Michael Bloomberg
Magajin garin New York Michael Bloomberg RFI

Kasar Amirka ta ankarad da jama’a don ayi hattara saboda ana iya amfani da cikan shekaru 10 da kai mata hari, a sake kai mata wani mummunan harin ta’addancin.Rahotanni daga New York na cewa yau Juma’a ‘yan sanda sun tsananta sintiri a Washington da kuma New York.Magajin garin New York Michael Bloomberg ya fadawa taron manema labarai cewa akwai kanshin gaskiya gameda yiwuwar kai masu hari wannan lokacin.Wasu majiyoyi daga fadar Shugaban kasar na cewa Shugaba Barack Obama ya bada umarnin yin kyakkyawan shiri domin gudun kada ayi masu sakiyar da ba ruwa.