Tasirin Cutar Maleriya

Sauti 10:00
Wani yaro a Uganda
Wani yaro a Uganda RFI

Cutar Maleriya cuta ce da ke cikin cutuka masu saurin kisan kananan yara, kididdiga ta nuna cewar kusan kowace daga cikin kasashen Nahiyar Afrika ana fama da wannan cutar da masana kiwon Lafiya suka tabbatar cewar ta samo asali ne daga cizon Sauro.Dangane da haka ne Faruk Muhammad Yabo ya yi mana nazarin tasirin cutar da yadda take zaman babbar barazana ga hukumomin a kasashen nahiyar Africa dama na hukumomin bada agaji na kasa-da-kasa.