EU

Kungiyar Tarayyar Turai zata bunkasa asusun ajiya

Reuters/François Lenoir

Kungiyar Kasashen Turai ta na shawarar ribanya kudaden dake asusun ajiyar ta na ko ta kwana zuwa Dala tiriliyon uku da rabi, dan fusknatar ko wane irin hali.Shugaban gudanarwar kungiyar, Jose Manuel Barroso ya bayyana haka, yayin da yake jawabi ga Majalisar kasashen Turai. Inda ya zasu karafafa sa ido da kuma kula wajen tafi da asusun, kuma dole asusun ya samu karfi, ya kuma fadada aikin sa, da kuma tabbatar da hadin kan dake tsakanin kasashen domin cimma biyan bukata.