Isra'ila-Palasdinawa

Israela Za Ta Saki Fursunoni Palestinawa 500

Manyan gobe Palestinawa na nuna halin da suke ciki
Manyan gobe Palestinawa na nuna halin da suke ciki RFI

Yau lahadi kasar Israela ta wallafa sunayen fursunonin 477 Palestinawa da zaa saki ranar jibi Talata, a wani matakin farko na yarjejeniyar sakin Sojan da aka kama Gilad Shalit.Jerin sunayen ya kunshi Palestinawa maza 450 da kuma mata 27, kamar yadda maaikatar Sharia ta kasar ta gabatar a shafin tan a yanar gizo.Bayanan na cewa akwai wasu fursunonin Palestinawa 550 da zaa saka nan da watanni biyu.