Niger

An yi Jana'izar tsohon Shugaban Jamhuriyar Nijar

Marigayi Janar Ali Saibou tsohon Shugaban kasar Janhuriyar Nijar
Marigayi Janar Ali Saibou tsohon Shugaban kasar Janhuriyar Nijar

A safiyar yau Laraba aka janaizar tsohon shugaban kasar Janhuriyar Nijar, Marigayi Janar Ali Saibu wanda ya rasu ranar Litinin data gabata 31 ga watan Oktoba 20011, a Yamai babban birnin kasar.Marigayi Janar Sabou ya rasu yana da shekaru71 da haihuwa bayan ya yi fama dadoguwar rashin lafiya.Abin mamaki a wurin jana'izar shi ne ga tsohon shugaban kasa Salou Djibo wanda ya yi wa Tandja Mamadu juyin mulki ya je ya gaida Tandja cikin fara'a hannun cikin hannu. Yayinda suke a jere Maman Usman, Tandja, Salou da kuma sabon shugaban kasa Alhaji Mahamadu Issoufou da sauran jiga jigan gwamnati da jami'an diplomasiyan kasashen duniya aka gudanar da zana'idar.Marigayi Janar Ali Saibou ya mulki kasar ta Janhuriyar Nijar dake yankin Yammacin Afrika daga shekarar 1987 zuwa shekarar 1993, inda ya girka tsarin demokaradiya mai jam'iyyu da yawa, sannan daga bisani ya tsame hanu daga cikin harkokin siyasa baki daya.