Cuba

Gwamnatin Kasar Cuba ta Amince da dokar saya da sayar da gidaje

Shugaban Cuba Raul Castro da Sakataren jam'iyyar Gurguzu mai mulki  Jorge Luis Tapia Fonseca
Shugaban Cuba Raul Castro da Sakataren jam'iyyar Gurguzu mai mulki Jorge Luis Tapia Fonseca Reuters/Enrique De La Osa

Gwamnatin kasar Cuba ta zartas da wata doka dake amincewa da mutane zasu iya saya ko saida gidajensu, a karo na farko cikin shekaru 50.Kamar yadda jaridu da mujallun kasar ke cewa wannan mataki na daga cikin matakan daidaita tattalin arziki da kuma tunkarar matsalar karancin gidajen kwana da ake fuskanta cikin kasra mai bin tsarin Gurguzu.