MDD

Wasu Likitoci sun gano yadda Cutar Sankara ke Sauyawa

Wasu Likitoci masu bincike sun ce sun gano yadda kwayoyin halittun gado na masu fama da cutar Sankara ko Cancer ke sauyawa, kuma hakan ya tamaka wajen yi wa masu cancer huhu magani.Likitocin Sun ce nasarar da suka samu kan wannan salon za su yi amfani da ita ga masu cancer nono da ta kwakwalwa kuma suna gwada ta kan masu cancer bargo da ake kira leukaemia.Sun ce abin da kawai suke so su cimma shine gano yadda ‘ya ‘yan hallitan gado ke canzawa da yadda ‘ya ‘yan jini ke yaduwa ba tare da an shawo kan su ba. Hakan na iya sa a gano ‘ya ‘yan halittar gadon masu kawo matsala a kuma magance su.