Liberiya

Shugaban Liberiya ta Sirleaf ta kafa kwamiti bincike

Reuters/Finbarr O'Reilly

Shugaban kasar Liberia Uwargida Ellen Johnson Sirleaf ta nada wata jagorar mata kiristoci domin shugabantar wani komitin musamman da zai binciki musabbabin harbin da ‘yan sanda suka yi lokacin da ‘yan adawan kasar ke zanga-zanga game da zaben kasar.Maccen Sister Mary Laurene Browne, 'yar shekaru 68 da haihuwa, wadda kuma malama ce a jami'a, zata shugabanci komitin binciken da aka yi makon jiya.Gwamnatin kasar na cewa mutun daya ne ya mutu amma kuma wasu kafofin na cewa sun fi haka.