Isa ga babban shafi
Turai

Poland ta nemi Mataki na bai guda kan Matsalolin Tattalin Arzikin Turai

REUTERS/Kacper Pempel
Zubin rubutu: Bashir Ibrahim Idris | Suleiman Babayo
Minti 2

Kasar Poland ta bukaci Babban bankin kasashen Turai da ya gaggauta saye kadarorin bankunan da basusuka suka yiwa katutu a Yankin, domin magance matsalar da kan iya jefa kasashen Turai cikin yaki.Ministan kudin Poland, Jacek Rostowski, da kasar sa ke jagorancin kungiyar kasashen Turai ya bayyana haka, inda yake cewa yanzu haka zabi biyu ya rage musu, ko a bada gagarumin tallafi, ko kuma a fuskanci yaki.Ministan ya ce, idan yau kungiyar kasashen Turai ta watse, zasu tafka asarar kadarorinsu, kuma hakan na iya haifar da matsalar tattalin arziki irin na shekarar 1930, wanda zai haifar da yaki a Turai.Ya kara da cewa, muddin aka kasa kwantar da hankalin kasuwanni, matsalar ba wai kawai zata tsaya a kasar Italiya ba, zata shiga sauran kasashe harma da kasar Jamus.Ya zuwa yanzu dai, wannan matsalar tattalin arzikin kasashen Turai ta lakume kujerun shugabanin kasashe uku, da suka hada da Italiya, Girka, da Spain. 

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.