Mutane 100 sun mutu a fadan satan shanu a Madagascar
Hukumomin a kasar Madagascar sun tabbatar da cewa wasu mazauna karkara a kudancin kasar, sun kashe akalla mutane 100 wadanda su ke zargin su ke sace musu shanu.Daya daga cikin manyan jami’an tsaron kasar, Laftanar Kanar Tahina Rakotomalala, ya shaidawa Kamfanin Dillancin labarn Faransa AFP cewa, mazauna karkaran sun kai harin na kwantar bauna, dauke da duwatsu, mashi da kibiyoyi da kuma bindigogi ne.
Wallafawa ranar:
A jiya dai aka bayyana cewa an kashe mutane akalla 67 wadanda ake su ma zargin cewa barayin shanu ne.
Haka kuma hukumomin kasar sun kara tabbatarwa da cewa, wasu mutane tara, cikinsu harda jami’ain tsaron farar hula biyu, Dan sanda daya da kuma wasu da ake zargin barayin shanu ne su shida.
Harin dai an kai shi ne kan wasu kauyuka da ke cunkushe a wuri daya a yankin, a yayin da wasu mutum biyu daga cikin kauyawan su ka samu raunuka
A yanzu haka dai an tsaurara matakan tsaro a yankin da lamarin ya faru, domin gudun kar a samu ramuwar gayya daga bangaren barayin shanun wadanda ake wa lakabi da Daholos.
A karshen makon nan ne mutanen karkaran su ka yi ikrarin an sace musu shanu, nau’in bijimi, wadanda su ke wa lakabi da Zebu, guda 100.
Rahotanni sun nuna cewa, an samu 98 daga cikin shanun.
A watan Yunin da ya gabata ne, aka tura jami’an tsaro a kudancin kasar ta Madagascar domin magance matsalar satar shanu wanda barayin kanyi da manya makamai.
Akan kuma samu mutuwar ‘Yan sanda a yankin inda aka taba kama wasu daga cikin barayin su kusan 100
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu