Najeriya

‘Yan fashin teku sun kwace wani jirgin mai na Singapore a Najeriya

Taswirar gabar Tekun Guinea
Taswirar gabar Tekun Guinea Wikipedia

Wasu ‘Yan fashin teku, sun kwace wani jirgin kasar Singapore wanda ke dauke da mai, a Jihar Legas, da ke kudancin Najeriya.Wannan fashi, shine na biyu da ya auku a cikin sati biyu da su ka wuce akan gabar Tekun Guinea, a cewar Hukumar ta Kasa da Kasa da ke kula da Tekun.  

Talla

Jirgin, a cewar hukumomi a birnin Kuala Lumpur, jirgin na dauke da mai ne, da kuma ma’aikata 23 a cikinsa.

Koda yake, hukumomin basu ba da bayanai akan yadda ‘Yan fashin tekun su ka kwace jirgin ba.

Sai dai shugaban hukumar, Noel Choong, ya ce sun sanar da hukumomin kasar ta Najeriya, kuma suna yin wani abu akai.

Choong ya kara da cewa “mu damuwar mu a yanzu, shi ne tsaron lafiyar ma’aikatan wadanda su ka kulle kansu a wani daki, da kuma yawan kwace jirage da ake yi a tekun”.

A watan da ya gabata, ‘Yan fashin tekun, sun kwace wasu jirage biyu a yankin Togo wadanda ke makil da mai, inda su ka kwashe man bayan sun kwace jiragen, wanda daga baya kuma aka sako jiragen tare da duk ma’aikatan.

A fadar Choong, wadanda su ka aikata wannan fashin su ne su ka kwace jirgin na Singapore, inda ya kara da cewa, “ yadda su ke yi, shine sai su je su juye man a wani jirgi su kuma yi wa jirgin kankat sannan sai su sake shi duk a cikin kwanaki biyar.”

Hukumar ta kasa da kasa mai kula tekun, ta sha yi wa jirage gargadi da su yi hattara a duk lokacin da su ke tafiya a kan gabar tekun yammacin Afrika, su kuma, jawo hankalin hukuma a duk lokacin da su ka fuskanci wata barazana.

An kai hare hare akalla sau 37 da su ka hada da kwace jirage, yin garkuwa da mutane, kisan kai, a wannan shekara, a yankin na gabar tekun Guinea.

‘Yan fashin dai su kan kwace jirage da ke dauke da kaya ne, musamman mai, inda su kan juye kayan a jirginsu su je su sayar a kasuwar bayan fage.

Kasar Najeriya da makwabaciyarta, ta Jamhuriyar Benin sun taba gudanar da wani shawagi a shekarar da ta gabata, a yunkurinsu na ganin cewa an magance matsalar fashin jirage.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.