Amurka

Obama ya amince da zama Dan takarar Jam'iyar Democrats a zaben Amurka

Shugaban Amurka Barack Obama ya amince ya yi tazarce a jawabin da ya gabatar na taron Jam’iyyar Democrats, shugaban kuma ya yi kira ga Amurkawa da su sake ba shi damar wasu shekaru hudu a fadar White house. Obama ya ce akwai bukatar Amurkawa su ba shi Karin wasu shekaru domin shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta da ya gina shekaru masu zuwa.

Shugaban kasar Amurka, kuma dan takarar Jam'iyar Democrats, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, kuma dan takarar Jam'iyar Democrats, Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

Ya kara da cewa zai magance matsalolin kasar tare da cimma bukatun kasar, inda ya kara da cewa, tafarkin da gwamnatinsa ta dauka zai iya bada wahala amma ita ce hanya madaidaiciya.

“Ina kira domin mu kare muradun kasarmu, da suka shafi makamashi ilimi da tsaro da tsare tsaren da za su samar da sabbin ayyukan yi tare da inganta tattalin arziki.” Inji Obama

Shugaban kuma, ya tabo batutuwa da dama da suka shafi nasarar kashe Osama Bin Laden da kuma yakin Afghanistan da ficewar Amurka daga Iraqi, sannan kuma ya soki abokin karawar shi Romney wanda ya ce bashi da tarbiyar diflomasiya.

A jiya ne dai, tsohon shugaban kasar Amurka Bill Clinton, ya yi kira ga Amurkawa, da su zabi Barack Obama karkashin jam’iyyar Democrat bayan ya bayyana goyon bayan shi ga shugaban a yakin neman zaben Jam’iyyarsu.

Clinton ya kuma kara da yin gargadin cewa jam’iyar Republican za ta jefa tattalin arzikin kasar cikin halin ni-‘yasu idan har ta kafa gwamnati.

A cewarsa, zaben Obama shi ne mafita ga tattalin arzikin Amurka, domin daidaita tattalin arzikin kasar da ya samu nakasu daga Gwamnatin George W. Bush da Obama ya gada.

Tsohon shugaban kasar ta Amurka, shi ne shugaba na farko da ya yi tazarce karkashin jam’iyyar Demokrat tun yakin duniya na biyu, shi kuma ne ya zabi Obama a matsayin dan takara.

Taron na ‘Yan Democrat, ya fara ne da wani bayani da Uwar gida, Michelle Obama ta yi a ranar Talata, a yayin da magoya bayan na Obama ke ta duruwa zuwa filin taron.

Clinton dai ya kasance har yanzu yana da farin jini a wurin Amurkawa kamar a lokacin da aka rantsar da gwamnatinsa a shekarar 1993 inda a wani binciken jin ra’ayin Amurkawa da gidan telebijin CNN ya gudanar, ya samu kashi 66.

A kuma cikin jawabinsa, Clinton ya kara fadawa Amurkawa dalilin da ya sa ba a so su zabi ‘Yan Republicans, inda ya yi zargin cewa, gwamnatin George W. Bush, wacce ta bar kan mulki shekaru hudu da su ka wuce, ta bar tattalin arzikin kasar cikin halin ni ‘yasu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI