Majalisar kasar Australia ta ki amincewa da kudirin dokar auren jinsi daya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Majalisar Kasar Australia ta ki amincewa da kudirin dokar auren jinsi guda da gagarumar rinjaye, inda ‘Yan Majalisu 98 suka kada kuri’ar watsi da dokar, wacce kuma ta samu goyan bayan ‘Yan Majalisu 42 kawai. Cikin wadanda suka kada kuri’ar watsi da dokar sun hada da Firaminista, Julia Gillard da shugaban ‘Yan adawa, Tony Abbott.
Ita dai Gillard ta ba wa ‘Yan majalisun dama ne su da su yi zabi akan abin da ya kamata ba amma ba a matakin Jam’iya ba.
Shugaban ‘Yan kwadago a majalisar, Anthony Albanese, wanda ya jefa kuri’ar goyon bayan kudurin dokar, ya ce duk da cewa kudurin ya sha ka yi a majalisa, kuri’u 42 da su samu na nuna cewa akwai kwarin gwiwa nan gaba.
“Shekaru kadan da su ka gabata, babu wanda ma zai yi tunanin kudurin dokar za samu goyon bayan kuri’u 42 a majalisar.” Inji Albanese.
Ya kuma kara da cewa “Sakamakon kada kuri’ar, ya nuna cewa akwai goyon bayan daga jama’ar kasar, ina kuma ganin cewa wata rana, ‘Yan majalisar za su gane hakan”
Kuri’ar da ‘Yan majalisun su ka kada dai ta kawo karshen muhawarar da aka kwashe makwannin ana yi, inda wani Dan majalisar Dattawa, ya kwatanta auren jinsi daya da saduwa da dabbobi, wanda hakan ya jawo cecekuce daga kuma kashe ya sa aka tilasta shi ya yi murabus saboda kalaman da ya yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu