Mali

Dakarun ECOWAS na shirye su kutsa kai cikin Mali - Rahoto

Rahotanni na nuna cewa, yanzu haka dakarun kungiyar kasahsen Afrika ta Yamma, wato ECOWAS da za suyi aiki a kasar Mali, na kasa, inda suke jiran umurnin kutsa kai zuwa cikin kasar. Kamfanin Dillancin labaran Faransa, ya jiyo daga Abidjan cewar, Najeriya da Faransa ne zasu bada kayan sojin da za’ayi amfani da su ta sama. 

dailynewsegypt.com
Talla

A Jiya ne, gwamnatin Mali ta bukaci tura sojin a gaban Majalisar Dinkin Duniya, a yayin da ake ganin ayyukan da dakarun za su yi a kasar ta Mali zai ki watanni biyu, domin ganin an fitar da ‘Yan tawayen kasar da su ke rike da Arewacin kasar.

Kasar Faransa wacce ta raini, Mali ta ce za ta taimaka wajen ba da wasu daga cikin gudunmuwar ababan da ake bukata, sai dai ba za ta bari dakarunta su kasance kan gaba wajen gudanar da ayyukan korar ‘Yan tawayen kasar ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI