Georgia

Al’umar Georgia na gudanar da zaben ‘Yan majalisu a yau

Wasu masu kada kuri'a na duba sunayensu a rumfunan zabe
Wasu masu kada kuri'a na duba sunayensu a rumfunan zabe

Yau al’ummar kasar Georgia ke gudanar da zaben ‘Yan Majalisu, wanda ake ganin zai zama zakarar gwajin dafin shugabancin Mikhail Saakashvilli, a kasar. Shugaban ‘Yan adawa, kuma wanda ya fi kowa kudi a kasar, Bidzina Ivanshvilli, ya zargi shugaban da kama karya, da kuma taka hakkokin jama’a, yayin da Shugaba Saakashvilli, wanda tun shekarar 2008 ke shugabancin, ke zargin ‘Yan adawan da yunkurin baiwa Russia damar tafi da al’amura a cikin kasar. 

Talla

Kasashen Amurka da yammacin Turai da ke marawa kasar ta Georgia baya sun yi kira da a gudanar da zabe mai inganci a kasar, inda su ka nanata cewa, mulkin Demokradiyya na da matukar muhimmanci ga cigaban kasar.

Masu saka ido akan zaben, kungiyar OSCE, sun kwatanta zaben a matsayin wanda zai iya samun tashin hankali a bayan zaben a kasar tag Georgia wacce ke dauke da mutane miliyan 4.5.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.