Sudan

Sudan ta nemi a yafe mata basussuka, a kuma tallafawa tattalin arzikinta

Shugaban kasar Sudan Omar Albashir
Shugaban kasar Sudan Omar Albashir

Kasar Sudan ta gabatar da bukatarta, a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya, na a yafe basussukan da ake bin kasar, har ila yau, a kuma tallafawa tattalin arzikinta, wanda ya shiga wani hali, bayan ta barwa, kasar Sudan ta Kudu, wani kaso mai tsoka, mai dauke da arzikin mai. A wannan satin ne, Hukumar bada Lamuni ta Duniya, IMF, ta nemi kasar ta Sudan da ta tattauna da masu tallafa mata tare da manyan Jami’an hukumar ta IMF, domin a san yadda za a rage bashin da ake binta, wanda ya kai kudi Dalar Amurka biliyan 40. 

Talla

Minsitan Harkokin Wajen kasar ta Sudan, Ali Ahmed Karti, a taron na Majalisar Dinkin Duniya ya ce, Sudan na bukatar taimako, a dai dai wannan lokaci mai sarkakiya, inda ya nemi da a yafe ma kasar basussukan da ake binta, aka kuma tallafawa tattalin arzikin kasar.

A dai watan Yulin bara ne, Sudan ta Kudu ta bangare daga kasar ta Sudan, wanda hakan ya sa kasar ta Sudan ta rasa wani muhimmin kason kudin shiganta, da ta kan samu ta fannin mai.

A kuma satin daya gabata ne, kasashen biyu suka saka hanu a yarjejeniyar tabbatar da tsaro akan iyakokinsu, sai dai har yanzu basu cimma matsaya ba, akan yankin Abyei wanda ke da muhimmancin ga kasashen biyu, saboda arzikin mai da yake dauke da shi da kuma wuraren kiwon dabbobi.

Kasar Amurka da sauren kasashen yammacin duniya sun dade suna sukar kasar Sudan, saboda zargin tauye hakkin Bil Adama da ake yi a kasar da kuma yadda ake gallazawa ‘Yan tawaye.

Har ila yau, Kotun manyan laifuka ta duniya ta samu shugaban kasar, Omar Albashir, da aikata laifukan yaki a Dafur, wanda hakan ya sa kasashen yammacin duniya su ka yi watsi da kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI