Somaliya

Dakarun hadin gwiwa na Afrika sun karbe Kismayo

Dakarun hadin gwiwa na Afrika
Dakarun hadin gwiwa na Afrika iamges.alarabiya.net

Dakarun Kungiyar kasashen Afrika ta AU, sun shiga cikin garin Kismayo, bayan nasarar da suka samu na korar ‘Yan kungiyar Al Shabaab daga birnin. Mazauna birnin sun ce, sun ga sojojin Kenya, wadanda suka jagoranci kama garin kwanaki biyu da suka gabata.Rahotanni sun ce anga dakarun kasar Somali wadanda suma su ke taimakawa wajen ganin an kori ‘Yan kungiyar ta Al Shabaab wadanda suka kwashe shekaru hudu sun a rike da yankin.  

Talla

Dakarun kasar Kenya sun isa Kismayo ne ta yammacin garin inda su ka kame wurare a garin.

Haka kuma wasu shaidu sun tabbatara wa da Kamfanin Dillancin labarai na AFP cewa dakarun Kenya wadanda su ka kwashe kwanaki biyu a wajen garin sun kasance a cikin dakarun hadin gwiwa wadanda yawansu ya kai 17,000.

Sai dia wasu shaidu sun ce su dakarun kasar Somalia kawai su ka gani.

“Wadanda na gani da ido na, sun kai kusan su 120, sanye da koren kaya na soja, amma banga dakarun kasar Kenya a cikinsu ba.” Inji wani mazaunin yankin, Abdirahman Said.

Masu saka ido akan rikicin na Kismayo sun bayyana cewa, korar ‘Yan Al Shabaab daga yankin zai hana su damar samun kayayyaki da su kan samu na taimako hade da kudaden da su kan samu wanda hakan ana ganin zai kawo karshen zamansu a yankin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI