UN

Adadin mutanen da ke fama da yunwa a duniya ya ragu, inji MDD

Wasu yara na murnar samun hatsin abinci
Wasu yara na murnar samun hatsin abinci

Majalisar Dinkin Duniya tace adadin mutanen dake fama da yunwa a duniya ya ragu daga miliyan 925 zuwa miliyan 870, amma duk da haka ba’a cimma bukatun yaki da yunwa a duniyar ba. Rahotan da hukumar samar da abinci ta Majalisar ta fitar yau, ya nuna cewar, bata gamsu da yawan mutanen dake fama da yunwar ba, duk da yake sun ragu zuwa miliyan 870 a fadin duniya daga miliyan 925, tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012.  

Talla

Hukumar tace a cikin kowanne mutane takwas da ake samu a duniya, mutum guda na fama da yunwa, inda shugaban hukumar, Jose Graziano da Silva, ke cewa, matakin ne da ba za’a amince da shi ba, yadda ake samun yaran dake da kasa da shekaru biyar miliyan 100 suna fama da rashin abinci mai gina jiki.

Shugaban hukumar yace, cigaban da aka samu a cikin shekaru biyu da suka gabata, ya zarce na baya, wanda suka samu saboda matsalar tattalin arzikin da duniya ta samu, hauhawan farashin kayayakin masarufi, bukatar yin man fetur da kayan abincin, da kuma fari a wasu sassan duniya.

Sai dai rahotan yace, yayin da ake samun cigaba a duniya, a nahiyar Afrika ba haka abin yake ba, inda mayunwatan suak karu daga miliyan 170 zuwa 234.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI