Amurka

Obama ya isa Jihar New Jersey

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya isa Jihar NewJersey fara ziyarar wuraren da mahaukaciyar guguwar Sandy ta yi barna a jiya. Wannan ziyara na zuwa ne a yayin da kasar ke shirin yin zabe a ranar Talata mai zuwa.  

Talla

Obama a cewar rahotanni na tare ne da Shugaban bada agajin gaggawa na kasar, Craig Fugate tare da gwamnan Jihar ta New Jersey, Chris Christie, wanda dan Jami’iyar Republikan ne.

Guguwar ta Sanday ta yi barna a kasar ta Amurka inda rahotanni suka ce akalla mutane 32 suka rasa rayukansu, a yayin da aka yi asarar dukiyoyin da suka kai kudi Dalar Amurka biliyan 20.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI