Venezuela

Shugaba Chavez na cigaba da samun sauki, inji Mataimakinsa

Wasu magoya bayan shugaba Hugo Chavez rike da hotunansa
Wasu magoya bayan shugaba Hugo Chavez rike da hotunansa REUTERS

Mataimakin Shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro, ya ce shugaba Hugo Chavez na samun karfin jiki, yayin da ya kammala murmurewa daga aikin da aka masa, kuma zai cigaba da wani sashe na neman lafiyarsa.

Talla

Maduro ya ce yanzu haka shugaban na samun sauki, kuma sassan jikin sa suna aiki, yayin da shugaban mai shekaru 58 ke farfadowa daga cutar sankarar da yake famar jinya a kasar Cuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.