Amurka

Amurka ta mika wani da ke tsare a Bagram ga hukumomin Mauritaniya

Amurkawa da ke adawa da barin gidan yarin Guantanamo a bude.
Amurkawa da ke adawa da barin gidan yarin Guantanamo a bude. Reuters/Larry Downing

A cikin wannan makon ne dakarun kasar Amruka suka mika wa kasar Mauritaniya wani danta, dan kungiyar Alka’ida da take tsare da shi a gidan yarin Bagram na kasar Afghanistan, ba na tsibirin Gwantanamon kasar Cuba ba, a cewar majiyar tsaron.

Talla

Ci gaba da tsare fursunonin da Amurka ta kama da sunan aikin ta’addanci kana take tsare da su a gidan yarin Gwantanamo, ba tare da yi masu shara’a ba, ya jawo ma ta suka mai yawan gaske a ciki da wajen kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI