Afghanistan

An samu baraka tsakanin Gwamnatin Afghanistan da Amurka

'Yan kungiyar Taliban a bukin bude ofishin a  kasar Qatar
'Yan kungiyar Taliban a bukin bude ofishin a kasar Qatar Reuters

Bisa dukkan alamu dai baraka ta fito fili tsakanin Gwamnatin Afghanistan da Amurka, kan shirin tattaunawar da suka shirya yi, wanda zai kaiga barin wasu jami’an sojin Amurka cigaba da zama a kasar. 

Talla

Shugaba Hameed Karzai ya zargi Amurka da harshen damo kan abinda take fada, da kuma wanda take yi a aikace, da kuma shirin ta na tattaunawa da kungiyar Taliban.

Rashin fahimtar junan ya biyo bayan bude ofishin kungiyar Taliban a kasar Qatar, wanda aka sanyawa suna Daular Musuluncin Afghanistan, wanda kungiyar tayi anfani da shi a karkashin mulkin ta daga shekarar 1996 har zuwa lokacin da aka hambarar da ita.

Kakakin Gwamnatin Afghanistan, Aimal Faizi,ya bayyana cewa shugaba Hameed Karzai bai amince da sunan ofishin ba, saboda baya cikin muradun kasar, kuma sun shaidawa hukumomin Amurka matsayin su.

Tuni dai shugaba Barack Obama yayi maraba da shirin tattaunawa da kungiyar ta Taliban, wanda Karzai ke ganin kamar barazana ce ga Gwamnatin sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI