RFI

RFI Hausa zai sauya Shafinsa na Intanet

Daga 15 ga watan Yuni, hausa.rfi.fr, shafin Intanet na RFI Hausa zai sauya sabuwar fuska, mai bayar da muhimmanci kan salon yada labarai irin na rediyo da hotunan bidiyo.

Fuskar sabon shafin RFI Hausa
Fuskar sabon shafin RFI Hausa RfI Hausa/Awwal
Talla

Sauyin da za a gani

Da farko siffar shafin. Akwai jan launi da tambarin RFI, launin baki domin kara kawata shafin. An bayar da muhimmanci ga hotuna, musamman wadanda aka sanya tare da rubutattun labarai, amma a wannan karon hotuna ne masu girma.

Shafin farko na jan hakali sannan ga haske. A duk lokacin da mutum ya shiga hausa.rfi.fr, mai karatu ko mai saurare zai tabbatar da cewa ya shiga shafin rediyo.

Saman shafin, na dauke da akwatin rediyo. Yana kunshe da alamar da ke ba da damar sauraren labaran RFI Hausa kai-tsaye da wadanda suka gabata. Saman Shafin na dauke da shirye-shiryen karshe na RFI Hausa.

A kasan alama mai kama da akwatin rediyo, za a tarar da alamu da ke yi wa mai karatu ko saurare jagora zuwa ga sauran shirye-shiryen RFI Hausa, tare da wasu sauye-sauye.

Nabigeshin, na iya motsawa daga sama zuwa kasa ko hagu zuwa dama ta hanyar amfani da wata alamar kibiya.

Manyan labaran hausa.rfi.fr. wannan karon an sauwake su fiye da tsarin tsohon shafin, za a tarar da labarai har goma sha biyu da aka wallafa a rana.

A kasan Shafin…..Za a tarar da Labaran wasanni. Da shirye-shiryen mako, da na karshen mako da kundaye kunshe da bayanai daban daban akan muhimman batutuwa da suka ja hankalin duniya.

A yi karatu lafiya!

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI