RFI

Yadda Za a yi hulda da RFI

© RFI/Sébastien Bonijol

Kana da gidan Rediyo ? Kana fatan watsa shirye-shiryen RFI ko kuma/ MCD ? A cikin wannan shafi kana iya samun cikakkun bayanai da za ka iya shiga sahun gidajen rediyo da ke hulda da RFI da MCD a sassa daban daban na duniya.

Talla

Me ake nufi da Rediyo abokin hulda?

Rediyo abokin hulda na nufin kafar yada labarai da ke watsa shirye-shiryen RFI ko kuma MCD a matsayin kyauta, ana iya watsawa kai-tsaye ko kuma a wani lokaci na daban a daya daga cikin harsuna 15. (Hausa, Larabci, Ingilishi, Faransanci, Kiswahili, Harshen Farisa, Cambodia, China, Sifaniyanci, Mandenkan, Fotuganci, Brazil, Romanci, Rashanci da harshen Vietnam).

Shirye-shiryenmu zuwa gare ku

• Labarai kan abubuwan da ke faruwa a duniya
Labaran duniya, labarai akai-akai, shirye-shirye, hirarraki da dai sauransu.

• Kida da waka masu kayatarwa daga sassan duniya

Wakoki

Kowane wata, RFI na samar da taurarin wakoki fiye da goma da aka zabo a cikin salo daban daban na mawaka (100 % Faransanci, Afirka, Hip-Hop, Musamman domin wannan wata, gwarzon RFI, RFI Vinyles, da sauransu…)

Za ku sami karin bayani game da labaran kida da waka a shafin http://www.rfimusique.com

RFI kida tsantsa

Kidan da ake amfani da shi don bude shirye-shirye, …RFI kida tsantsa da yawansu ya kama daga 25 zuwa 30 domin inganta shirye-shiryenku. Domin karin bayani sai a shiga shafin http://www.rfi-instrumental.com

• Shirye-shirye cikin harsuna biyu domin koyon Faransanci

Kuna iya ba masu saurarenku damar inganta magana da harshen Faransanci, ta hanyar gabatar ma su da shirin tattaunawa a cikin harshe biyu.

Ko ta yaya? Shiri ne da aka tsara shi domin koyon Faransanci a sauwake. Domin karin bayani sai a ziyarci shafin: https://savoirs.rfi.fr/fr/ecouter-nos-cours-de-francais

Ta yaya za ka zama abokin hulda da RFI?

Ya zama wajibi ka sanya hannu kan yarjejeniya.

1) Shiga shafinmu na Intanet domin cikewa tare da aikewa zuwa wannan adireshi: http://partenariat.rfi.fr (Gargadi: za a cike ne a wadannan harsuna, Faransanci, Ingilishi, Sifaniyanci ko kuma harshen Portugal.)

2) Idan har RFI ta amince da bukatar da ka gabatar, za a samu bayanai a game da sauran batutuwa da suka shafi wannan yarjejeniya.

Gargadi: kafin watsa shirin RFI ko kuma MCD a tasharku, ya zama wajibi a tabbatar da cewa hakan bai sabawa dokokin kasarku ba.

Ta yaya za a iya kama shirye-shiryen RFI ko MCD, bayan kulla yarjejeniya?

Ta satellite
Kamawa kai-tsaye : A tauraron Dan Adam da ke amfani da tasharku, za a kama mu kyauta ne a daya daga cikin taurarin da muke watsa shirye-shiryenmu.

Lalabo tasharmu kai-tsaye a tauraron Ordispace (Saboda Afirka kawai) : ta amfani da ‘wata na’urar da RFI za ta ba ka, za ka kama shirye-shiryenmu da Ordispace, na zamani (da aka girka cikin shekara ta 2016).

Ta Intanet
Kamawa kai-tsaye/ ko bayan an watsa : Kana iya samun dukkanin shirye-shiryen RFI/ ko MCD kai-tsaye, sauke shirye-shirye daga sashen raba shirye-shirye, ta hanyar amfani da kalmarka ta sirri don shiga: www.programmes.rfi.fr.

Ina za a kama RFI ?
Za ka samu karin bayani a game da yadda ake kama RFI da MCD a tashoshinmu na FM, ta gidajen rediyo abokannin huldarmu da sauran hanyoyin da aka saba kama mu: http://www.rfi.fr/contenu/capter-rfi

Mu kasance a tare (akan sashenmu na Afirka kawai)
Domin kasancewa tare da RFI da kuma sauran gidajen rediyo abokan huldarsa, sai a kasance da mu a shafinmu na Facebook a shafin RFI rediyo abokannin hulda a ciki, za ka nemi samu shafin mahawara na RFI da sauran gidajen rediyo abokan hulda a Afirka (ba da sauran jama’a ba).

Tuntube mu
Idan kuna da tambaya/ ko neman karin bayani, sai ku tuntubi shugaban sashen kula da wannan sashe a yankinku a wannan adireshi:  radiospartenaires@rfi.fr

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.