Bakonmu a Yau

Shekaru shida da barkewar rikicin Syria

Wallafawa ranar:

Shekaru shida cur da barkewar boren al’umma da ke nuna fushi dangane da yadda shugaban Bashar Assad ke tafiyar da mulkin kasar Syria, boren da daga bisani ya rikide zuwa yakin basasa.Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana rikicin na Syria a matsayin mafi muni tun bayan kammala yakin duniya na biyu, inda aka samu asarar rayukan mutane sama da dubu 320, yayin da wasu milyoyi suka gudu suka bar gidajensu.Dakta El-harun Muhammad, masani siyasar kasashen Yankin Gabas ta Tsakiya, ya bayyana wa Bashir Ibrahim Idris mahangarsa dangane da wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa.

Hari a garin al-Izaa kusa da birnin Aleppo na Syria
Hari a garin al-Izaa kusa da birnin Aleppo na Syria Reuters/路透社