Amurka-China-Koriya

Trump ya ce za a iya warware rikicin Koriya a diflomasiyance

Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping.
Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na China Xi Jinping. REUTERS/Jonathan Ernst

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashen China da Rasha da su taka rawar da ta dace domin warware rikicin nukiliyar Koriya ta Arewa, inda ya ce lokaci na neman kure wa kasar.

Talla

A taron manema labaran da ya gabatar karshen ganawarsa da shugaban Xi Jinping, shugaba Trump ya ce China ce ta fi dacewa domin warware wannan rikici a cikin sauki kuma a gaggauce fiye da kowace kasa.

Shugaban na Amurka ya jinjina wa Xi Jinping dangane da matakan takaita kasuwanci tsakanin kasarshi da Koriya ta Arewa sakamakon barazanar da kasar ke yi wa duniya da makamanta na nukiliya.

Bayan ganawar tasu, shugaban Trump ya ce akwai yiyuwar za a iya warware rikicin na Koriya a diflomasiyance.

Trump na shirin ganawa da shugaban Rasha Vladimir Putin a taron APEC da zai gudana a gobe juma’a a Vietnam, inda ake sa ran zai yi amfani da wannan dama domin neman goyon bayan Rasha don daukar matakai a kan kasar ta Koriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.