Amurka

Yan Democrat za su kalubalantar hukuncin Obamacare

Shirin inshoran lafiyar Obamacare na Amurka
Shirin inshoran lafiyar Obamacare na Amurka ®https://www.flickr.com/photos/ladawnaspics/

Wani alkali a Amurka ya bayyana shirin inshoran lafiyar da aka yiwa lakabi da Obamacare a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulki.Hukuncin alkali Reed O’Connor na zuwa ne kwana guda kafin sanya hannu kan shirin na shekarar 2019 domin ganin ya zama doka.

Talla

Hukuncin ya harzuka ‘ya’an Jam’iyyar Democrat wadanda a karkashin mulkin su ne aka kaddamar da shi,lokacin shugaba Barack Obama na jagorancin kasar, kafin shugaba mai ci Donald Trump ya soke shi.

Jam’iyyar Democrat tace zata daukaka kara kan hukuncin har sai taje kotun koli, inda alkalai 5 daga cikin 9 da suka goyi bayan shirin a shekarar 2012 har yanzu suke kan kujerar su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.