Isa ga babban shafi
Isra'ila

Mai yiwuwa a kafa gwamnatin hadaka a Isra'ila

Fira Minista mai ci Benjamin Netanyahu, da kuma ta Blue and White ta Benny Gantz
Fira Minista mai ci Benjamin Netanyahu, da kuma ta Blue and White ta Benny Gantz 路透社。
Zubin rubutu: Abdoulaye Issa
1 Minti

Mai yiwuwa zaben Isra’ila da ake ci gaba da dakon sakamakonsa, ya kai ga shiga tattaunawar kafa gwamnatin hadin gwiwa tsakanin manya da kuma kananan jam’iyyun kasar, la’akari da cewar ana tafiya kan-kan-kan tsakanin manyan jam’iyyun.

Talla

Lamarin na zuwa ne bayan da sakamakon farko na akalla kashi 90 na kuri’un da aka kidaya yanuna cewar har yanzu ana tafiya ne kan-kan-kan tsakanin jam’iyyar Likud ta Fira Minista mai ci Benjamin Netanyahu, da kuma ta Blue and White ta Benny Gantz, inda a yanzu kowanne ya lashe kujeru 32 a zaben ‘yan majalisar kasar da ake ci gaba da tattara sakamakonsa.

Masu bibiyar zaben na Isra’ila sun kuma yi hasashen cewar jam’iyyar Fira Minista Netanyahu a karshe za ta lashe kujeru 56, yayinda ta Gantz za ta sami 55, abinda zai gaza adadin kujeru 61 da kowanne ke nema don samun rinjayen kafa gwamnati, kuma a gefe masu hasashen suka ce kawancen kananan jam’iyyun kasar guda 4, za su lashe kujeru 12, daga cikin jimillar kujerun majalisar guda 120.

Rahotanni daga Isra’ilar na cewa mai yiwuwa sai a gobe Alhamis hukumar zaben kasar za ta bayyana cikakken sakamako, saboda tsaurara matakan kidaya kuri’un da aka kada.

Kusan kashi 69 da rabi na masu zabe a Isra’ilar ne suka kada kuri’a a zaben majalisar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.