Kasashen duniya sun hana shisshigi a rikicin Libya
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Taron da shugabannin kasashen da ke da hannu a rikicin Libya suka gudanar a birnin Berlin na kasar Jamus, ya bukaci a kawo karshen shisshigin kasashen ketare a wannan rikici, tare da tsaurara takunkuman hana shigar da makamai a kasar ta Libya.
Kasashe 11 ciki har da Rasha da Turkiyya ne suka halarci taron a karkashin jagorancin Majalisar Dinkin Duniya, to sai dai ba kamar yadda aka zata ba, Firaminista Fayez al-Sarraj da Khalifa Haftar ba su yi ganawar keke da keke a lokacin wannan taro ba.
Shugabar gwamnatin Jamus mai masaukin baki Angela Markel, ta ce taron ya yi ittifakin cewa dole bangarorin da ke da hannu a rikicin su mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a ranar 12 ga wannan wata na Janairu, yayin da aka bukaci bangarorin biyu da su kafa kwamitin da zai sa-ido kan aiwatar da yarjejeniyar da zai kunshi mutane 10 dukaninsu sojoji, biyar daga kowane bangare.
Domin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar, majiyoyin Majalisar Dinkin Duniya sun ce, za a gayyaci wakilan kwamitin domin su halarci wani taro da zai gudana a ranakun 28 da 29 ga wannan wata a birnin Geneva.
Babban aikin da ya rataya a wuyan wannan kwamiti shi ne kokarin hada kan rundunonin sojin kasar tare da kwance damarar mayakan sa-kai. To sai dai jim kadan bayan kammala taron na birnin Berlin an ci gaba da ji karar harbe-harbe a kudancin birnin Tripoli.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu