Amurka-Trump

Majalisar Dattijan Amurka ta wanke Donald Trump daga tsigewa

Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa gaban Majalisar wakilai.
Shugaban Amurka Donald Trump yayin jawabinsa gaban Majalisar wakilai. REUTERS/Leah Millis/POOL

Majalisar Dattijan Amurka ta wanke shugaba Donald Trump daga tuhumar da Majalisar wakilai ta masa na karya ka’idodin aiki guda biyu da kuma bukatar tsige shi daga mukamin sa.

Talla

Majalisar Dattijan wadda 'yan Jam’iyyar Republican ta shugaba Trump ne ke da rinjaye a cikinta ta wanke shugaban da kuri’u 52 da 48 a tuhumar farko kan karya ka’idar aiki.

A bangare guda dangane da tuhumar da akewa Donald Trump kan yunkurin hana majalisa aikinta, shugaban na Amurka ya samu nasara a zauren majalisar da kuri'u  53 da 47 matakin da ya bayar da cikakkiyar damar wanke shi.

Tuni dai sanarwar da majalisar ta fitar cikin daren jiya Laraba wayewar yau Alhamis ta sanar da watsi da karar wadda jam'iyyar Democrta marar rinjaye a majalisar ta fitar.

Sanarwar ta bayyana gaza samun shugaban da laifukan da ya cancanci tsigewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI