Coronavirus

Fiye da Mutum Miliyan 8 Coronavirus ta kama a sassan Duniya- WHO

Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar lafiya ta Duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus. Christopher Black/OMS/Handout via Reuters

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce adadin mutanen da cutar coronavirus ta kama a sassan duniya ya zarce miliyan 8, kuma sama da rabi sun fito ne daga Amurka da nahiyar Turai.

Talla

Hukumar Lafiyar ta WHO ta ce alkaluman da ta tattara ya nuna mata cewar ya zuwa yau Talata mutum miliyan 8 da dubu dari 2 da 2 suka kamu da cutar coronavirus a kasashen duniya, yayin da ta kashe mutane dubu 435 da 176 galibinsu a Amurka da Turai.

A cewar WHO a Nahiyar turai kadai akwai mutum miliyan 2 da dubu 417 da dari 9 da 2 wadanda suka kamu da coronavirus yayinda ta ke da jumullar mutum dubu 188 da 85 da cutar ta kashe tun bayan barkewarta.

WHO ta kuma bayyana yadda ake da mutum miliyan 2 da dubu 110 da dari 182 da Coronavirus ko kuma COVID-19 ta kama a Amurka ciki kuwa har da mutum dubu 116, da 81 da cutar ta kashe.

Hukumar ta ce adadin masu kamuwa da cutar ya ribanya tun daga ranar 10 ga watan Mayu, yayin da a cikin kwanaki 10 da suka gabata aka gano mutane sama da miliyan guda da ke dauke da cutar.

WHO ta bayyana yiwuwar karuwar adadin masu dauke da cutar da adadi mai yawa la'akari da cewa sai yanzu ne wasu kasashen duniya suka fara gudanar da gwajin cutar ta coronavirus.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI