Amurka

An bukaci Biden ya dauki bakar fata mataimakiyarsa a zaben Amurka

Wasu fitattun bakaken fata sama da 100 da ke kasar Amurka sun bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran Jam’iyyar Democrat a zabe mai zuwa Joe Biden mace bakar fata a matsayin wadda za ta mara masa baya a fafatawar da za su yi da shugaba Donald Trump a watan Nuwamba mai zuwa.

Joe Biden,dan takara a zaben shugaban Amurika daga jam'iyyar democrat
Joe Biden,dan takara a zaben shugaban Amurika daga jam'iyyar democrat ANDREW CABALLERO-REYNOLDS / AFP
Talla

Fitattun mutanen sun hada da Reverend William Barber da mai gabatar da shirye shirye Charlamagne Tha God inda suke cewa kin daukar shawarar na iya yi wa takarar Biden illa.

Mutanen sun ce an dade ana bukatar mata bakaken fata su taka rawa wajen yakin neman zabe da zaben kansa wajen goyan bayan Jam’iyyar Democrat ba tare da an mutunta su ko karrama su ba.

A wasikar da suka rubuta wa Biden, mutanen wadanda suka hada da Benjamin Crump sun ce bukatarsu wani goyan baya ne, bayan irin wannan wasikar da fitattun mata bakaken fata 700 suka rubuta wa dan takarar a makon jiya.

Bangarorin biyu sun bayyana bacin ransu kan yadda ake sukar matan da ke gaba gaba wajen neman mukamin da suka hada da Sanata Kamala Harris da tsohuwar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Susan Rice.

Sauran matan da ke neman mukamin sun hada da 'yar Majalisar wakilai Karen Bass da Val demings da suke bakaken fata, sai kuma Turawa sanata Elizabeth Warren da Tammy Duckworth tare da Gwamnan Michigan Gretchen Whitmer.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI