Hotunan taron Kwaminisanci na China

Shugaban China Xi Jinping tare da mahalarta taron koli na jam'iyyar gurguzu mai mulki REUTERS/Thomas Peter

Taron koli na jam’iyyar gurguzu da ke mulki a China, ya tsawaita wa’adin shugaban kasar Xi Jinping da shekaru biyar a nan gaba, tare da tabbatar da shi a matsayin shugaba mafi daukaka da kasar ta taba samu a baya-bayan nan. Maharta taron, sun jefa kuri’ar ne a asirce a yau laraba, tare da tabbatar da firaministan kasar Li Kegiang da wasu mutane biyar a matsayin mambobi a kwamitin koli na jam’iyyar.

Talla