Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Google da Microsoft sun amince da matakin dakile hotunan batsa

Sauti 10:17
Alamar kamfanin Microsoft da ke kera na'urorin sadarwa
Alamar kamfanin Microsoft da ke kera na'urorin sadarwa REUTERS/Dado Ruvic
Da: Awwal Ahmad Janyau

Manyan kamfanonin injunan bincike a Internet Google da Microsoft sun amince da bukatar daukar matakan samar da tarko da zai dakile yada hutunan tsaraici musamman na kananan yara da ake keta hakkinsu. Dangane da wannan batu ne shirin na ilimi yi yi nazari akai.

Talla

Matsalar yada hutunan batsa na kananan yara ta kafar Intanet matsala ce da gwamnatocin manyan kasashe suka kaddamar da yaki da ita musamman Birtaniya da Amurka.

Haka yasa manyan kasashen biyu suka nemi kawancen kamfanonin leken asiri domin farautar mutanen da ke yada hutunan na batsa a kafar Intanet.

kamfanin Google yace ya samar da wata sabuwar fasaha da zata dakile duk hotunan batsa na akalla masu binciken hotunan sama da 100,000.

Amma yunkurin da Google da Microsoft suka yi na daikle hotuna da bidiyon batsa na kananan yara, ya shafi kasashe ne masu Magana da harshen Ingilishi, amma kamfanonin biyu sun ce zasu fadada fasahar nan da watanni shida ga sauran harsuna a duniya kusan 158.

Matakin dai na wadannan manyan kamfanonin binciken na Intanet na zuwa ne kwanaki kalilan bayan ‘Yan sandan Canada sun cafke mutane sama da 300 a sassa daban daban na duniya da suka hada da malaman makaranta da likitoci da ke yada hutunan batsa na kananan yara kasa da shekaru 5. Kuma mutanen da aka cafke sun kunshi ‘yan kasashen Canada da Latin Amurka da Afrika da Turai da Asiya.

wannan dai duk ya shafi hanya ce ta bincike da ke bayar da saukin kai wa ga hutunan da aka saka na batsa a Intanet cikin lokaci kalilan, amma akwai dimbin hanyoyi da dama da ake yadawa tare da musayar hotunan batsa.

Wadatuwar samun hanyoyin sadarwa na aika sako a wayoyin salula irin 2go da Whatapps da kuma Blackberry, hanyoyi ne kuma da wasu ke amfani da su domin yadawa da musayar hutunan batsa a tsakaninsu musamman tasakanin mace da namiji ko kuma ‘Yan madigo da ‘Yan luwadi, al’amarin da suke yi asirce tsakaninsu idan har wayarsu ta salula tana hade da intanet.

Haka ne dai masana suke ganin duk da cewa matakan da Google da Microsoft suka dauka mataki ne mai kyau na dakile yadauwar hutunan batsa, amma kuma akwai hanyoyi da dama da ake bi domin kaucewa binciko hotunan ta hanyar bincike a Google ko Microsoft.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.