Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Sabulun wanke wayar Salula

Sauti 10:17
Na'urar sabulun wanke  wayar salula da ake kira Phonesoap a turance da aka samar inda kuma mutum kuma zai iya cajin waya.
Na'urar sabulun wanke wayar salula da ake kira Phonesoap a turance da aka samar inda kuma mutum kuma zai iya cajin waya. Digital trend
Da: Awwal Ahmad Janyau

Shirin ilimi Hasken Rayuwa ya yi bayani ne game da bajekolin fasaha da aka kammala a ranar juma’a da aka gudanar a Las Vegas a kasar Amurka. a cikin shirin zaku ji wata sabuwar na’ura da ake kira sabulun wanke wayar salula da aka samar saboda dimbin cututtukan da aka gano waya na duake da su.

Talla

A duk shekara ne dai ake gudanar da kasuwar bajekolin fasaha a watan Janairu a birnin Las Vegas da ke jahar Nevada a kasar Amurka.

Bajekolin dai tamkar gasa ce ake yi tsakanin kamfanonin kere keren fasaha, inda suke guzurin sabbin kayayyaki da suka kera tare da bayar da sanarwar wata sabuwar fasaha da ake shirin kaddamarwa anan gaba.

Akwai kamfanin Google da samar da masarrafar Android da zai dasa a motocin zamani karkashin wani kawance tsakanin Kamfanin da kamfanonin kera motoci da suka hada da Honda da Hyundai da Audi.

Google dai yana kokarin samar da hurumi ne ga masu amfani da wayoyin zamani da ake kira Smartphones don su sauya masarrafarsu ta Android zuwa ga akwatin telebijin da ke gaban motarsu, idan har sun mallaki irinta.

Masarrafar Android dai yanzu ta bazu a duniya musamman a wayoyin salula na Smartphones inda akalla akwai sama da biliyan da ke amfani da massarafar a wayoyin salula da wasu bangaorirn fasaha na daban.

Tuni dai Kamfanin kera motoci na BMW a Jamus suka kulla irin wannan kawancen da kamfanin Apple da ke hammaya da Android.

A 2013 dai alkalullma sun ce kasuwar fasaha a duniya ta haura sama fiye da kudi sama da dala Trillion daya kuma kasuwar ta cira ne saboda kasuwar wayoyin zamani na Smartphones.

Shirin ya zanta da masana game da wannan batu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.