Isa ga babban shafi
Ilimi Hasken Rayuwa

Manhajar da ke gano an saci Fasahar wani

Sauti 09:43
Wasu masu aiki da Kwamfuta a Turai
Wasu masu aiki da Kwamfuta a Turai REUTERS/Morris Mac Matzen
Da: Awwal Ahmad Janyau

Shirin Ilimi Hasken rayuwa na wannan makon ya yi bayani ne game da manhajar da ke yaki da satar Fasaha musamman daga dalibai da marubuta wadanda ke mallake fasahar wani ba tare da ambato sunan marubuci ba. Shin ko ya girman matsalar take a makarantu? Ko matsalar ta fi kamari yanzu saboda samun wadutuwar Intanet? Wadannan sune batutuwan da shirin ya yi nazari akai.

Talla

A wani bincike game da satar fasaha da aka gudanar, Alkalumman binciken sun ce an samu karuwar matsalar da kashi 10 a tsawon shekaru 10 da suka gabata, inda aka bayyana Kwamfuta da Intanet a matsayin wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen sawwaka satar Fasaha a zamanin nan.

Yawanci dai dalibai yanzu sun dogara ne da Intanet saboda saukin zurfafa bincike, tare da sawwaka wa masu bincike kai wa ga ayyukan wasu.

Idan dai marubuci ko dalibi ya yi amfani da aikin wani marubuci ba tare da ambato sunan shi ba, hakan laifi ne.
 

Shirin ya tattauna da Masana game da girman Matsalar a duniya da Najeriya da Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.