Ilimi Hasken Rayuwa

Brazil: fasahar tantance kwallo a raga

Sauti 10:10
Na'urar tantance kwallo a raga
Na'urar tantance kwallo a raga Reuters/Wolfgang Rattay

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa ya yi bayani ne game da sabuwar Na’urar tantance kwallo a raga da aka fara amfani da ita a karon farko a gasar cin kofin duniya a Brazil. Zamu ji abubuwan da ke kunshe da na’urar da muhimmacinta

Talla

Wannan ne karon farko da aka fara yin amfani da fasahar tantance kwallo a raga a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil, kamar yadda ake amfani da fasahar a filayen wasannin da ake gudanar da gasar Premiership ta Ingila.

A karon farko na’urar ta fara aiki ne a gasar cin kofin duniya a wasan da Faransa ta lallasa Hunduras ci 3-0.

A baya dai kafin nazarin samar da na’urar, akan samu cece-kuce, musamman Franck Lampard na Ingila zai yi na’am da sabuwar fasahar wanda aka haramta wa kwallon shi a ragar Jamus a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a Afrika ta kudu a shekara ta 2010.

To akwai dai wata na’ura daure a hannun alkalin wasa kamar Agogo, idan har aka samu kwallo a raga da zata iya canyo cece-kuce, a nan take ne cikin dakika, alkalin wasan zai iya gani a hannunsa ko kwallon ta keta layin ragar kafin ya yanke hukuncin an ci.

Shirin ya tattauna da Zubairu Sani, mataimakin alkalin wasa ne na Hukumar FIFA daga Najeriya da kuma masanin Fasahar Sadarwa Umar Saleh Gwami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.