Isa ga babban shafi
Rasha

‘Yan sama jannati sun sauka lafiya a Kazakhstan

International Space Station crew members
International Space Station crew members REUTERS
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Wasu ‘Yan sama jannati guda uku sun sauko lafiya a kasar Kazakhstan a jiya Alhamis bayan shafe lokaci suna jiran tsammani a sararin samaniya sakamakon matsaloli da suka fuskanta daga bangaren Rasha. Dirowar mutanen lami lafiya a doron kasa ya ja hankalin duniya musamman a shafukan Twitter a Facebook.

Talla

‘Yan sama jannatin guda uku sun sauka doron kasa lafiya ba tare da wata tangarda ba kuma cikin koshin lafiya.

Mutanen uku sun hada da Dan kasar Rasha da wata ‘Yar kasar Italiya da Ba’amurke, kuma sun sauka ne a Kazakhstan bayan sun shafe tsawon wata a sararin samaniya suna jiran tsammanin makomar dawowarsu a doron kasa sakamakon matsaloli na tsaiku da aka samu daga bangaren hukomin Rasha wajen ba su damar sauka a doron kasa.

Tun a watan Mayu ne dai ya kamata ace sun sauko kasa, lamarin da ya sa saukar a jiya ya ja hankalin duniya don ganin sun sauka lafiya.

Mutanen guda uku sun shafe kwanaki 200 a sama jannati.
Kuma Matar da ke tare su ita ce yanzu mace ta farko a tarihin mata da suka yi yawan kwanaki a sama jannati.

Wannan al’amari dai ya sa matar mai suna Cristoforetti, yanzu ta yi fice a duniya inda cikin lokaci kankani ta samu miliyoyan mabiya a shafin Twitter.

Mutanen dai sun tafi yawon bincike kimiya da fasaha ne a sama jannati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.