Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya tattauna ne game da sauye-sauyen da kafar sada zumunta ta Facebook ke shirin aiwatarwa don in dadin masu amfani da kafar bayan caccakar da Kamfanin na Facebook ya sha na tatsar bayanan sirrin mutane miliyan 50 a lokacin yakin neman zaben shugaban Amurka Donald Trump a 2016. Sai dai Facebook din ya bada hakuri tare da fadin cewa, ya zama dole ya wayar da kan al'umma kan yadda za su sauya abin da suke so cikin sauki.
Sauran kashi-kashi
-
Ilimi Hasken Rayuwa Ilimi Hasken Rayuwa, na magana kan halin da karatun yara yan gudun hijira ke ciki a Nijer A wannan makon Shamsiya Haruna ta duba yadda gwamnatin jamhuriyar Nijar ke kokari wajen samarwa yara yan gudun hijira guraban karatu a cikin makarantun bokon kasar gudun kar su yi biyu babu, ba gida ba kasa ba kuma Ilimi.23/05/2023 10:01
-
Ilimi Hasken Rayuwa Karancin dakunan karatu na barazana ga karatun Firamare a Neja Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna ya mayar da hankali kan kalubalen da karatun Firamare ke fuskanta a jihar Neja ta tsakiyar Najeriya, dai dai lokacin da ake samu karuwar yaran da ke zuwa makaranta.16/05/2023 09:59
-
Ilimi Hasken Rayuwa Ko yaya makomar karatun daliban da aka kwashe daga Sudan take? Shirin na wannan rana, ya duba halin da karatun daliban da suke tsere daga Sudan ke ciki, yayin da rikici ya barke a kasar da ke gabashin Afirka.09/05/2023 10:02
-
Ilimi Hasken Rayuwa Najeriya za ta fara kwashe daliban kasarta da ke Sudan zuwa Masar Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce sun fara tattaunawa da mahukuntan kasar Masar a birnin Alkahira, kan yadda za a kwaso daliban kasar daga Sudan, yayin da bangarori biyu ke ci gaba da gwabza yaki a kasar da ke Gabashin Afirka.25/04/2023 09:58
-
Ilimi Hasken Rayuwa An yaye daliban farko da suka koyi aikin likita a jami'ar Damagaram Shirin 'Ilimi Hasken Rayuwa' ya yi tattaki zuwa jihar Damagaram Zendir ta Jamhuriyar Nijar ne, inda jami'ar Damagaram ta yaye daliban farko da suka yi karatun aikin likita. A wannan jami'ar, kuma a wannan rana aka gudanar da bikin karrama malaman sashen koyar da kiwon lafiya da suka samu karin girma, sakamakon nasarar da suka yi ta cin jarabawar kwarewar nan ta hukumar kula da kwarewar malaman jami'o'i a nahiyar Afrika.28/03/2023 09:55