Bakonmu a Yau

Farfesa Abdallah Uba kan karrama Najeriya a fagen ilimi

Sauti 03:25
National Open University of Nigeria. (NOUN)
National Open University of Nigeria. (NOUN) The Guardian Nigeria

Hukumar Kula da ilimi, al’adu da kimiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware kowacce ranar 8 ga watan Satumba a matsayin ranar yaki da jahilci, in da ake nazarin kokarin da ake na tabbatar da cewar kowanne Bil Adama ya samu ilimi. Wannan ya sa an gudanar da bukukuwa a birnin Paris in da aka karrama kasashe 5 kan rawar da suke takawa wajen harkar bada ilimi, cikinsu har da Najeriya in da aka karrama Budaddiyar Jami'ar Najeriya, wato NOUN da ake karatu a gida da kuma hukumar gidan yarin kasar. Bayan bikin, Farfesa Abdallah Uba Adamu, shugaban Jami’ar ta NOUN ya yi Bashir Ibrahim Idris karin bayani.