Faransa-Najeriya

Jami'o'in Faransa na zawarcin daliban Najeriya

Darektar Tsangayar Kula Harkokin Ilimin jami'o'in Faransa a Najeriya, Charline Fouchet
Darektar Tsangayar Kula Harkokin Ilimin jami'o'in Faransa a Najeriya, Charline Fouchet RFI/Hausa

Faransa ta kaddamar da gagrumin aikin wayar da kan daliban Najeriya da zummar gayyato su domin neman ilimi a jami’o’in da ke sassan kasar ta Faransa.

Talla

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Turai ke ci gaba da bullo da tsare-tsaren takaita kwararar baki.

Darektar Tsangayar Kula da Harkokin Ilimin Jami'o'in Faransa a Najeriya, Charline Fouchet ta shaida wa RFI hausa cewa harshen Faransaci ba zai hana daliban Najeriya karatu a Faransan ba.

A cewar Fouchet, a halin yanzu akwai fannonin ilimi dubu 1 da 500 da ake koyar da su a harshen Turancin Ingilishi, kuma  babu bukatar daliban su kware a harshen Faransanci kafin samun guraben karatu a Faransa

"Mun yi amanna cewa, dama ce gagaruma a je Faransa saboda mutum zai iya neman iliminsa a harshen Turanci ba tare da fuskntar turjiyar yare ba." In ji Fouchet

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Abdurrahman Gambo

Jami'o'in Faransa na zawarcin daliban Najeriya

A halin yanzu dai, akwai hulda tsakanin tsangayar da gwamnatin jihar Kano, inda a kowacce shekara ake samun dalibai kimanin 10 da ke balaguro zuwa Faransa domin karatun digiri na biyu ko kuma na uku.

Wadannan dalibai na amfanar da al'ummar Najeriya ta hanyar da su a jami'o'in Kano da zaraan sun dawo gida Najeriya. In ji Fouchet wadda ta jagoranci taron manema labarai da ya gudana a Cibiyar Koyar Harsehn Faransanci ta Mike Adenuga da ke birnin Lagos.

Mafi tarin lokuta akan zargi daliban Afrika da aikata ta’asa a yayin da suke karatu a nahiyar Turai, amma a cewar Rafiu Omoleye, wakilin tsangayar ilimin Faransa a Najeriya, ba su taba samun labarin wani dalibin Najeriya da ke aikata manyan laifuka ba.

Omoleye ya ce, babban kalubalen da daliban ke kokowa da shi, shi ne rashin iya magana da harshen Faransanci a yayin da suka samu kansu a tsakiyar Faransawa a kasuwanni ko shaguna ko kuma unguwanni da makamantansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.