Ilimi Hasken Rayuwa

Matashin da ke amfani da hannun batir a Gombe

Sauti 10:00
Zubairu Yusha'u lokacin da aka yanke hannayensa
Zubairu Yusha'u lokacin da aka yanke hannayensa RFI/ Saulawa

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya waiwayi labarin yaron nan mai suna Zubairu Yusha'u da aka yanke wa hannaye bayan sun rube sakamakon daure su da malaminsa na makarantar allo ya yi a jihar Gomben Najeriya. Tuni gwamnati ta dauki nauyin Zubairu zuwa kasar India, inda aka yi masa hannayen da ke aiki da batiri. Kuna iya latsa hoton labarin domin jin yadda Zubairu ke sarrafa hannayensa na batiri.