Masu kalaman batanci za su biya Naira miliyan 5 a Najeriya kashi na 2

Sauti 10:12
Ministan Yada Labarai na Najeriya Lai Mohammed.
Ministan Yada Labarai na Najeriya Lai Mohammed. REUTERS/Afolabi Sotunde

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon tare da Bashir Ibrahim Idris ya yi nazari kan matakin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta dauka na yi wa dokar yada labarai kwaskwarima, inda ta kara yawan kudin tarar da ake cin masu kalaman batanci daga Naira dubu 500 zuwa Naira miliyan 5.