Saves the Children-Ilimi

Kungiyar Saves the Children ta koka da yadda corona ta hana yara karatu

Wasu daliban Makaranta a birnin Nairobi na kasar kenya.
Wasu daliban Makaranta a birnin Nairobi na kasar kenya. REUTERS - THOMAS MUKOYA

Kungiyar Agaji ta ‘Saves the Children’ ta bayyana damuwa kan yadda miliyoyin yara a fadin duniya suka gaza samun ilimin da ya dace a makarantu sakamakon matakan da hukumomi suka dauka na rufe makarantu domin yaki da cutar korona.

Talla

Rahotan da kungiyar ta fitar yau ya ce irin wadannan dalibai sun yi asarar akalla kashi daya bisa uku na kwanaki 190 da ake bukatar su samu ilimi a makarantu, inda ta bukaci gwamnatoci da masu bada agaji da su dauki matakan gaggawa domin shawo kan lamarin.

Kungiyar agajin ta ce irin wadannan matakai sun saka daliban sun yi asarar kwanaki 74 na samun ilimi kamar yadda alkaluman da Hukumar UNICEF da Majalisar Dinkin Duniya suka nuna.

Daraktan kungiyar Inger Ashing ta bukaci ganin ba’a sake fuskantar irin wannan matsala a shekarar 2021 ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.