Ilimi-Duniya

Yau kasashe ke bikin ranar Malamai ta Duniya

Wasu malamai a Habasha.
Wasu malamai a Habasha. ASHRAF SHAZLY AFP

Kowacce ranar 5 ga watan Oktoba na matsayin ranar Malamai a sassa daban daban kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta ware don girmamawa ga malaman da kuma tuna irin gudunmawar da suka bai wa Al'umma baya ga lalubowa tare da magance matsalar da bangaren ilimi ke fuskanta.

Talla

Kamar kowacce shekara a wannan karon ma ranar Malaman ta bana ta mayar da hankali kan yadda za a habaka irin gudunmawar da malaman ke bai wa al'umma tare da dakile matsalolin da ke tunkaro harkokin ilimi a matakai daban-daban.

Taken ranar Malaman na bana shi ne ''Malamai a tubalin farfado da ilimi daga nakasu'' taken da ke nuna bukatar da ake da shi ta hada hannu wajen farfado da harkokin ilimi musamman a kasashen da ke fuskantar koma baya a fannin karatu.

Annobar cutar corona ta taka muhimmiyar rawa wajen haddasa koma baya a harkokin karatu musamman a kasashe masu tasowa wadanda suka gaza amfani da tsarin bayar da ilimi ta yanar gizo bayan dokar kulle a kokarin yaki da cutar.

Haka zalika bikin na bana wanda UNESCO kan jagoranta ya koka da yadda miliyoyin yara kan gaza samun ingantaccen ilimi a kasashen da ke fama da rikici, kama daga ta'addanci da rikicin kabilanci da 'yan bindiga da masu tayar da kayar baya.

Kasashen yammacin Saharar Afrika na jerin wadanda ilimi ke samun koma baya, musamman bayan tsanantar matsalolin tsaro masu alaka da hare-haren ta'addanci da 'yan bindiga da kuma 'yan aware da sauran tsirarun mayaka da ke fafutuka daban-daban a kasashe irin Najeriya, Nijar Kamaru, Mali Chadi da kuma Burkina Faso.

Haka zalika wasu bayanai na nuna yadda ilimi ya matukar samun koma baya a Habasha, musamman yankin Tigray inda 'yan tawaye ke ci gaba da fada da sojojin gwamnatin kasar wanda ya tilasta dakatar da harkokin karatu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI