Ilimi Hasken Rayuwa

Fasahar Harba Kumbo A Kaduna

Wallafawa ranar:

Shirin ILIMI HASKEN RAYUWA ya tattauna da Mallam Shehu Saleh Balami, matashi dan shekaru 28 wanda yasamu nasarar kerawa tare da kuma harba rocket, wato kumbo a sararin samaniya a Jihar Kaduna a Nijeriya. Shidai Mallam Shehu ya kammala karatu digire na farko a fannin kimiya da fasaha a jami'ar kimiya da fasaha ta tarraya a Minna, Jihar Nijer a shekara ta 2008.Ya samu nasarar harba rocket din a ranar 27 ga watan Fabirairu ta 2011.