Ilimi Hasken Rayuwa

Shiri Akan Satar Bayanan Sirrin Kamfanin Sony a Yanar Gizo

Sauti 10:03

A kwanan nan ne kamfanin Sony mai kera na’urorin Video da Telebijin da abun daukar hoto da dai sauransu ya sanar da cewa wasu sun shiga gurbin na’urar kamfanin ta wasanni waton Play station3 a turance da ake bugawa a yanar gizo, inda kamfanin ya yi gargadin cewa wasu sun shiga ta yanar gizo sun saci bayannan sirrin mutanen da ke mu’amula da su. Sama da mutane biliyan 70 ne a duniya ke amfani da na’urar wasannin ta Sony domin buga wasannin a yanar gizo tare da tatso wasu wasannin zuwa ga kwamfutarsu domin buwaga ba lalle sai a yanar gizon ba.Idan har dai mutum zai fara mu’amula da kamfanin na Sony to dole sai ya gabatarwa da kamfanin wasu bayanan da suka shafe shi musamman suna da adreshi da ranar haihuwa hadi da bayanan sirrin da suka shafi katin cirar kudi wato credit card.To sai dai wasu barayin fasahar kwamfuta sun samu shiga na’urar, tare da sace bayanan sirin na mutane, har ma da kudaden ajiyarsu ta bankuna. bayan kwashe kwanaki ne kamfanin ya dauki matakin toshe kafar,Akan wannan batu shirin “Ilimi Hasken Rayuwa” ya tattauna da Y Z Ya’u, Directan gudanarwa na Cibiyar Bunkasa Na’urar kwamfuta a Nigeria. ko yaya ya ke kallon wannan al’amari da har wasu suka samu hanyar cimma naurar kamfanin na sony a yanar gizo ba tare da sanin kamfanin ba?